Vidic ya ce ba zai bar Manchester ba

Vidic
Image caption Dan kwallon Manchester United Nemanja Vidic

Dan kwallon baya na Manchester United Nemanja Vidic ya ce baida niyyar barin kungiyar.

Dan shekaru 28 da haihuwa, Vidic an yita rade rade akan cewar zai bar United kafin kakar wasan da za a fara nan da 'yan kwanaki

Vidic"Jita jita ce kawai ake yadawa, amma bani da niyyar barin United".

Vidic dai ya koma United ne a shekara ta 2006 akan pan miliyan bakwai daga kungiyar Spartak Moscow