Ba za a fara Premier da Carrick ba

Michael Carrick
Image caption Michael Carrick yana cikin tawagar Ingila ta gasar cin kofin duniya

Manchester United ta tabbatar da cewa dan wasanta na tskaniya Michael Carrick, ba zai buga wasannin farko na gasar Premier da za a fara ba. Carrick ya samu rauni ne a wasan da Manchester ta doke wata kungiyar kasar Ireland da ci 7-1 ranar Laraba.

Manajan Manchester Sir Alex Ferguson, ya ce dan wasan mai shekaru 29, "ba zai taka leda na wasu satuttuka ba."

"Michael ya samu rauni a idan sahunshi. Raunin ba shi da tsanani amma ba zai buga wasannin farko na kakar bana ba," a cewar Ferguson. Wannan raunin dai na nufin dan wasan ba zai taka leda a wasan da Manchester za ta kara da Chelsea ba, na neman cin kofin Community Shield, wanda za a yi ranar Lahadi. Da kuma wasanta na farko na gasar Premier da za ta buga da Newcastle a ranar 16 Agusta.