Ina nan daram a Arsenal: Fabregas

Fabregas na nan daram a Arsenal
Image caption Fabregas yana taka rawar gani sosai a Arsenal

Kyaftin din Arsenal Cesc Fabregas, ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a kungiyar, duk da aniyar da ya nuna abaya ta komawa Barcelona.

Dan wasan mai shekaru 23, an dade ana danganta shi da Barcelona bayan da aka kammala kakar wasanni ta bara, kuma sau biyu Arsenal tana kin amincewa da tayin Barcelona kan dan wasan.

Fabregas ya nemi afuwa daga magoya bayan kungiyar ta Arsenal abisa lokacin da ya dauka kafin ya fayyace matsayinsa a kungiyar.

"Ni kwararren dan wasa ne, kuma na fahimci bukatar Arsenal ta kin sayar dani," a cewar Fabregas.

"Akwai nauyin da ya rataya akaina na kociyanmu da 'yan wasa da kuma magoya baya, don haka zan mutunta hukuncinsu, kuma yanzu zan maida hankali ne kan ciyar da Arsenal gaba".

Dan wasan ya samu tarba ta musamman lokacin da ya koma horo tare da sauran takwarorinsa a filin wasa na Emirates a ranar Alhamis.