Mido na shirin barin Middlesbrough

Mido
Image caption Mido

Kocin Middlesbrough Gordon Strachan ya shaidawa Mido da Marvin Emnes da kuma Didier Digard da cewar baya bukatarsu a kakar wasan bana.

An yan wasan uku dai sun dawo horo kungiyar, amma Strachan ya ce yana da isasun 'yan wasa a kungiyar domin haka baya bukatar su.

"Ina da kwarin gwiwa cewar akwai kungiyoyin da za su bukace su a Turai"

Boro dai ta sayi Digard ne a kan fam miliyan hudu daga kungiyar Paris Saint Germain a Faransa, da kuma Emnes a kudi fam miliyan 3.2 daga kungiyar Sparta Rotterdam a watan Yulin shekarar 2008, a yayinda kuma Mido ya zo kungiyar daga Tottenham Hotspur a kudi fam miliyan 6 a watan Agusta shekarar 2007.