Appiah ya koma kungiyar Cesena ta Italiya

Appiah
Image caption Kaptin din Ghana Stephen Appiah

Kaptin din Black Stars na Ghana Stephen Appiah ya kulla yarjejeniya da kungiyar Cesena ta Italiya daga tsohuwar kungiyarshi Bologna.

Dan shekaru 28 da haihuwa, Appiah ya kulla yarjejeniya ta shekara guda tare da kungiyar kuma yana da damar sabunta yarjejeniyar.

Appiah yace "Na ji dadin kulla yarjejeniya da Cesena saboda ta nuna sha'awarta akaina tun lokacin da muka fara tattaunawa".

Appiah wanda ya takawa Black Stars leda a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu, a watan daya wuce ne ya bar Bologna bayan shafe watanni shida tare da ita saboda bambamci akan sabon kwangila.

Cesena ta kasance kungiya ta shida a gasar Serie A ta Italiya da Appiah ya kulla yarjejeniya da ita, bayanda ya bugawa Udinese da Parma da Brescia da Juventus da kuma Bologna.