Ivory Coast za ta nada Gerarrd Gili a matsayin Koci

Drogba da Gili
Image caption Drogba da Gili lokacin gasar cin kofin Afrika a 2008

Ivory Coast na tattaunawa da tsohon kocin Marseille Gerrard Gili akan batun daukar shi haya a matsayin sabon mai horadda 'yan kwallon kasar.

Ivory Coast dai bata da koci tun bayan kamalla gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu inda aka fidda ta tun a wasan zagayen rukuni.

Saboda dalilai na kudi hukumar kwallon kafa ta kasar wato FIF dai ta kasa cigaba da aiki da Sven Goran Eriksson wanda ya jagoranci 'yan kwallon kasar zuwa Afrika ta Kudu.

Shugaban FIF din Jacques Anouma ya ce yanasaran Gili zai iya zama ingantaccen mai horadda 'yan kwallon kasar.