Martin O'Neill ya yi murabus a matsayin kocin Aston Villa

O Neill
Image caption Tsohon Kocin Aston Villa David O Neill

Aston Villa ta sanarda cewa kocin 'yan wasanta Martin O'Neill ya yi murabus daga mukaminshi ba tare da bata lokaci ba.

A ranar litinin ne O'Neill ya bada sanarwar a yayinda Aston Villa ke shirin bude gasar premier ta bana tsakaninta da West Ham a karshen mako.

A cewar kungiyar Kevin MacDonald zai zama kocin riko na kungiyar kafin a nada sabo.