Bayern Munich ta takawa Faransa birki akan Ribery

Ribery
Image caption Frank Ribery

Bayern Munich ta ce ba zata bar dan kwallonta Frank Ribery ya je Faransa don sauraron ba'asi akan dalilan da suka sanya Faransa bata taka rawar gani ba a gasar cin kofin duniya.

Bayern a ranar litinin tace ba zata amince sammacin da hukumar kwallon kasar Faransa ta baiwa Ribery don ya gabatar da bayanai a ranar 17 ga watan Agusta a birnin Paris.

A cewar kungiyar, hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayyana kuru kuru a dokokinta cewar kungiyoyi zasu iya barin 'yan kwallo zuwa kasashensu ne kawai idan har 'yan kwallon zasu buga kwallo ne ba wai don wasu dalilai ba.

Shugaban Bayern Karl-Heinz Rummenigge shine ya bayyana matsayar kungiyar a wata wasika daya aikewa shugaban hukumar kwallon Faransa Duchaussoy.