Adebayor na tunanin dawowa tawagar Togo

Emmanuel Adebayo
Image caption Emmanuel Adebayo

Emmanuel Adebayor zai iya dawowa takawa Togo leda idan mahukunta a kasar sun cimma wasu daga cikin bukatun shi.

Dan wasan mai takawa kungiyar Manchester City leda ya yi marabus daga takawa kasar shi leda, bayan harin da aka kai musu a gasar cin kofin Afrika da aka yi a Angola a watan Junairun daya gabata.

"Idan abubuwa suka gyaru, zan dawo takawa Togo leda". In ji Adebayo, a hirarsa da mujallar kungiyar City.

"A gaskiya bana jin dadin daina takawa kasa ta leda, matakin dana dauko ya yimin ciwo, idan har idan suka daidaita al'amura a kasar zan dawo".

Adebayor nada mahimmanci a tawagar kasar Togo amma wasu a baya sun zargi dan wasan da kitsa rashin jituwa tsakanin 'yan wasan kasar.