Usain Bolt ya samu rauni

Usain Bolt
Image caption Usain Bolt

Shahararren dan tseren nan Usain Bolt ba zai sake tsere ba a bana saboda raunin da ya samu a bayan sa.

Tyson Gay ya doke Bolt a tseren mita dari da aka yi a gasar Diamond League a birnin Stockholm dake Sweden a ranar shida ga watan Agusta.

"Shekarar 2011 da Shekarar 2012 suna da muhimmanci a rayuwa ta, kuma ina fatan zan murmure a kan lokaci domin ci gaba da tsere". In ji Bolt.

Bolt ba zai samu damar tsere a gasar Diamond League da za yi a Zurich da Brussels.