Jamus za ta lashe gasar cin kofin duniya a 2014

Joachim Loew
Image caption Joachim Loew da 'yan kwallon Jamus a Afrika ta Kudu

Kocin Jamus Joachim Loew ya ce yanasaran 'yan kwallon kasarshi su lashe gasar cin kofin duniya a Brazil a shekara ta 2014.

Loew yace"Mun yi aiki don tabbatar da cewar a nan gaba abubuwa zasu inganta, ina tunanin cewar a shekara ta 2014 zamu daga kofin".

Bayan da Michael Ballack da Simon Rolfes da Heiko Westermann suka fasa zuwa Afrika ta Kudu saboda rauni, sai Loew ya tafi da matasan 'yan kwallo wadanda basu goge ba amma sai suka bada mamaki.

Sabbin 'yan kwallo kamarsu Manuel Neuer da Mesut Ozil da Sami Khedira da Thomas Muller aka hadasu da Philipp Lahm da Bastian Schweinsteiger da Lukas Podolski kuma sai kwallayi ta biya kudin sabulu.