Koriya ta Kudu ta doke Najeriya daci biyu da daya

Super eagles
Image caption Tawagar 'yan kwallon Najeriya

Super Eagles na Najeriya ta sha kashi a wajen takwaratta na Koriya ta Kudu daci biyu da daya a wasan sada zumuncin da suka buga.

Koriya ta Kudun ce ta fara zira kwallo minti 17 da fara wasan inda Yoon Bit-Garam yaci.

Osaze Odemwingie ne ya farkewa Najeriya kwallon bayan da Kalu Uche ya more kwallon, a yayinda Choi Hyo-Jin yaci wa Koriyar kwallonta na biyu.

Najeriya da Koriya ta Kudu dai sun tashi biyu da biyu a gasar cin kofin kwallon duniya a Afrika ta Kudu a watan Yunin daya wuce.

Haka zalika, kocin daya jagoranci Super Eagles zuwa Afrika ta Kudu wato Lars Lagerback a makon daya gabata ne yaki amince ya cigaba da kasance mair horadda 'yan kwallon kasar.