Manchester United ta sayi dan Portugal Bebe

Ferguson
Image caption Kocin United Sir Alex Ferguson

Manchester United ta sayi dan kwallon Portugal Bebe daga kungiyar Vitória de Guimarães.

Dan shekaru 20 da haihuwa, Bebe ya shafe makwani biyar a Guimarães kafin United ta fara farautarshi.

Rahotanni sun nuna cewar Kocin Manchester Sir Alex Ferguson ya biya akalla pan miliyan bakwai akan dan kwallon.

A baya dai Real Madrid ta soma zawarcin Bebe kafin ya sasanta da United.

Bebe ya kasance dan kwallo na takwas da United ta sayi kafin a soma kakar wasan bana.