An sabunta: 12 ga Agusta, 2010 - An wallafa a 13:51 GMT

Rayuwar kwallon kafan Beckham cikin hotuna

David Beckham cikin hotuna

 • David Beckham
  Kocin Ingila Fabio Capello ya ce ba zai dauki David Beckham domin takawa tawagar kasar leda kuma ba.
 • David Beckham
  Kocin ya ce yana son ya rika amfani da 'yan wasan da shekarun su, ba su kai na David Beckham ba wanda yake da shekarun haihuwa 35.
 • David Beckham
  An dai tambayi Capello shin ko Beckham na cikin tsare tsaren shi nan gaba sai ya ce; "a'a ba zan kara kiransa ba, David dan wasa ne kwararre amma ina ganin muna bukatar sabin jini ne a tawagar kasar."
 • David Beckham
  Capello ya ce Beckham zai iya bugawa Ingila wasa guda a filin Wembley domin ya yi ban kwana da 'yan kallo.
 • David Beckham
  Kocin dai ya ce bai tattauna da Beckham ba game da makomarsa, amma ya ce idan dan wasan ya samu isashen lafiya zaiyi amfani da shi a wasa guda.
 • David Beckham
  Capello dai ya furta wadannan kalaman ne bayan Ingila ta doke Hungary a wasan sada zumunci da suka buga a filin Wembley, a wasan da kasar ta buga na farko, bayan mumunar rawar data taka a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu.
 • David Beckham
  David Backham tare da matarsa Victoria.
 • David Beckham
  Theo Walcott da Adam Johnson ne suka buga a bangaren da Beckham ke bugawa a hannun dama, kuma sun haskaka a wasan.
 • David Beckham
  Tsohon kyaftin din Ingila Beckham ya bar ingila ne ya koma kungiyar Los Angeles Galaxy a Amurka a shekarar 2007, kuma dan wasa ya takawa Ingila leda sau 115.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.