Liverpool ta sayi Poulsen daga Juventus

Poulsen
Image caption Danish Midfielder Christain Poulsen

Liverpool ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Denmark Christian Poulsen daga kungiyar Juventus akan pan miliyan hudu da rabi.

Poulsen mai shekaru 30 da haihuwa zai kasance tare da Liverpool har zuwa shekara ta 2013.

Zuwan Poulsen alamace ta zai maye gurbin Javier Mascherano wanda ya bayyanawa Manajan Liverpool Roy Hogson cewar yanason ya bar Anfield.

A halin yanzu dai Poulsen ya hade da sauran sabbin 'yan kwallon Liverpool wato Joe Cole da Milan Jovanovic da Jonjo Shelvey da Danny Wilson.

Poulsen a baya ya taka leda a Schalke da Sevilla sannan kuma ya bugawa Denmark wasa sau 77.