Chelsea za ta kare kofinta na gasar Premier-Ancelotti

Ancelotti
Image caption Kocin Chelsea Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce kungiyarshi zata kare kofinta na gasar premier bayan da Chelsea din ta lallasa West Brom da ci shida da nema a makon farko na gasar.

A lokacin karawar dai Didier Drobga ya zira kwallaye uku shi kadai a yayinda Flourent Malouda yaci biyu sai Frank Lampard wanda yaci kwallo daya.

Ancelotti yace"Mun yi aikin daya dace damu na cin kwallaye da dama".

A lokacin wasannin share fage na fara kakar wasa na bana dai Chelsea bata ji dadi ba, infa ta sha kashi wajen Ajax da Eintracht Frankfurt da Hamburg, sannan kuma Manchester United ta doke ta a wasan Community Shield.