Ba za muyi gaggawar sayar da Liverpool ba

Liverpool
Image caption Dubban magoya bayan Liverpool a filin Anfield

Manajan Darektan kungiyar Liverpool ta Ingila Christian Purslow ya shaidawa BBC cewar ba za ayi gaggawar sayarda kungiyar ba.

A cewar shi dukda yake akwai kamfanoni da dama da suka rubuto tayinsu na mallakar kungiyar, amma dai mahukunta kungiyar na takatsantsan don kada su fuskanci matsaloli.

Ya kara da cewar har yanzu 'yan Amurkan nanne wato Tom Hicks da George Gillett ke mallake da kungiyar Liverpool din.

Christain Purslow ya ce burin kungiyar a kakar wasa ta bana shine ta samu gurbi a gasar zakarun Turai.

"A kakar wasan da aka fara dai, zamu maida hankali don ganin cewar mun tsallake zuwa gasar zakarun Turai, saboda muna da zaratan 'yan kwallo" In ji Purslow.