Dan Senegal Mamadou Niang ya koma Fernebache

Niang
Image caption Dan kwallon Senegal Mamadou Niang

Dan kwallon Senegal Mamadou Niang ya bar kungiyar Marseille ta Faransa ya koma Fenerbache ta Turkiya.

Niang dai shine ya fi kowanne cin kwallaye a Marseille inda ya zira kwallaye 18 kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar Faransa a karon farko tun shekarar 1992.

Koda yake dai Marseille bata so barin Niang ya tafe ba,amma dai yarjejeniyar ana saran ta kai dala miliyan goma.

Kocin Marseille Didier Deschamps ya ce"tafiyar Mamadou zata shafi makomar kungiyar gaba dayanta".