Al Ahly ta shiga tsaka me wuya a kwallon Afrika

Al Ahly
Image caption 'Yan kwallon Al Ahly dana JS Kabilye

Kungiyar JS Kabilye ta Algeriya ta samu maki tara bayan ta doke Al Ahly ta Masar daci daya da nema a wasan zakarun kwallon Afrika.

Mohammed Khourti Ziti ne ya ci kwallon a minti na 25, abinda kuma ke nufin cewar har yanzu babu kungiyar data samu galaba akan JSK a rukuni na biyu.

Ahly dai a yanzu tafi Ismaili da maki guda, bayan da Ismaili din ta doke Heartland ta Najeriya daci daya me banhaushi.

Wannan kashin da Heartland ta sha a wajen Ismaili din ya janyowa kungiyar ta Najeriya babbar matsala na iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba.