Carrick ya gargadi 'yan kwallon Manchester United

Rooney
Image caption Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney

Michael Carrick ya ce dole ne sai 'yan kwallon Manchester United sun guji kuskure a baya, don kada su fuskanci matsala a wasansu na farko na gasar premier tsakaninsu da Newcastle.

A kakar wasan data wuce dai an doke Manchester United sau takwas abinda kuma ya sanya Chelsea ta lashe gasar premier.

Carrick ya gargadi sauran 'yan Manchester United cewar ba zai wuyi su bari a kara shiga gabansu a Ingila ba"

A cewar Carrick din yana saran Newcastle ta fito da karfinta gannin cewar a wannan karon ne ya kara dawowa gasar premier.