Ba ma son James Milner ya bar Aston Villa

Milner
Image caption James Milner na Aston Villa

Dan kwallon Aston Villa Stewart Downing ya ce basa son James Milner ya koma Manchester City.

Downing ya ce idan har Milner ya koma, to basu da wanda zai maye gurbinshi.

Milner dai yaci kwallo daya a wasan da Villa ta lallasa West Ham United daci uku da nema.

Downing yace"Idan ya tafi, muna mashi fatan alheri, amma idan har ya zauna munsan cewar zamu amfana dashi".

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya nuna kwadayin sayen Milner amma har yanzu basu sasanta tsakaninsu da Aston Villa ba.