Andy Murray ya ce zai lashe gasar US open

Murray
Image caption Andy Murray yana murnar doke Roger Federer

Dan Britaniya Andy Murray ya ce zai iya lashe gasar US open bayanda a ranar lahadi ya daga kofin Rogers can a Toronto.

Murray wanda shine na hudu a fagen tennis a duniya ya doke Roger Federer ne daci 7-5, 7-5 a wasan karshe, kofin da ya zama mishi na farko a bana.

Murray yace"babban buri na a yanzu shine lashe gasar US open kuma wannan nasarar ta zama zakaran gwajin dafi".

A ranar 30 ga watan Agusta ne za a fara gasar US Open.

Akan hanyarshi ta daga kofin Rogers dai, Murray ya samu galaba akan Roger Federer da Rafael Nadal da kuma David Nalbandian.