Anelka ya yiwa hukumar kwallon Faransa gwalo

Anelka
Image caption Nicolas Anelka ya ce hukumar kwallon Faransa ta yi shirme

Nicolas Anelka ya ce abin ya bashi dariya da hukumar kwallon kafa ta Faransa FFF ta dakatar dashi na wasanni 18 saboda yadda ya gudanar da kanshi a gasar cin kofin duniya.

A Afrika ta Kudu dai kocin Faransa Raymond Domenech ya kori Anelka mai shekaru 31 da haihuwa gida.

Anelka ya shaidawa France Soir cewar "duka abin shirme ne kawai, saboda sabon koci Laurent Blanc na bukatar zaman lafiya da 'yan kwallo ne".

Ya kara da cewar"mutanen nan 'yan wasan kwaikwayone,dariya za ta kashe".

Anelka yace dakatar dashi ba zaiyi wani ta siri ba, saboda a tunaninshi yayi ritaya daga bugawa Faransa kwallon tun a ranar 19 ga watan Yuni.