Craig Bellamy ya koma Cardiff City

Bellamy
Image caption Mancini yana yiwa Bellamy a dabo

Craig Bellamy ya koma kungiyar Cardiff City na wucin gadi daga kungiyar Manchester City.

Dan shekaru 31 da haihuwa, Bellamy ya ce "Naji dadin dawowa gida Cardiff".

Mai horadda 'yan kwallon Cardiff Dave Jones yace kawo Craig cikin kungiyar babbar nasara ce garesu.

Bellamy dai ya taka leda a kungiyoyi takwas daban daban akan kusan pan miliyan 45 kuma tuni kocin Manchester City Roberto Mancini ya nuna cewar ba zai yi da Bellamy.