Dan Indiya zai sayi Blackburn Rovers ta Ingila

Blackburn
Image caption Magoya bayan Blackburn Rovers

Blackburn Rovers ta ce tayi tattaunawa mai armashi tsakaninta da hamshakin dan kasuwan Indiya Ahsan Ali Syed akan batun sayarda da kungiyar.

Tuni dai dan kasuwan wanda ke zaune a Bahrain ya tabbatar da cewar ya zaku ya sayi Blackburn din.

Ali Syed dai ya ce zai baiwa kocin Blackburn Sam Allardyce pan miliyan 100 don ya sayi 'yan kwallo.

A cewar mahukunta kungiyar daga nan zuwa makwani biyu za a kamalla yarjejeniyar.

Rahotanni dai sun nuna cewar Syed me shekaru 36 da haihuwa zai saye Blackburn ne akan pan miliyan 300 wanda kuma ya isa a biya bashin da ake bin kungiyar da kuma sayen sabbin 'yan kwallo.