An nada Javier Clemente a matsayin kocin Kamaru

Clemente
Image caption Sabon Kocin Indomitable Lions Javier Clemente

An nada tsohon kocin Spain Javier Clemente a matsayin sabon mai horadda 'yan kwallon Indomitable Lions na Kamaru.

Dan shekaru 60 da haihuwa ya maye gurbin Paul Le Guen wanda ya sauka bayanda aka doke Kamaru a duka wasanninta uku a gasar cin kofin duniya.

A baya dai Clemente yayi jagoranci Spain a shekarar 1992 zuwa 1998, sannan ya je Serbia daga shekara ta 2006-2007.

Tsaffin 'yan kwallon Kamaru biyu Fran├žois Omam-Biyik da Jacques Songo'o ne zasu zama mataimakanshi.

Sanarwar da Ministan wasannin kasar Michel Zoah ya fitar bata bayyana tsawon shekarun da zai shafe ba.

Wani jami'in hukumar kwallon kafa ta Kamaru FECAFOOT ya shaidawa BBC cewar Clemente zai zo Kamaru a mako mai zuwa don a kulla yarjejeniyar.