An kama Joe Cole yana sharara gudu a mota

J Cole
Image caption Dan kwallon Ingila Joe Cole

An gargadi dan kwallon Liverpool Joe Cole akan cewar za a iya kwace mashi lasisin tuka mota, idan har aka kamashi da laifin sharara gudu akan titi.

Dan shekaru 28 da haihuwa, an kama Cole a cikin motarshi kirar Audi A4 yana matukar gudu a Claygate, Surrey.

Cole yaki amincewa da laifin kuma bai halarci zaman kotun Majitire din ba.

Alkalin kotun Clive Wilves ya daga sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Agusta, kuma ya ja kunen Cole cewar zai iya rasa lasisinshi na tuki.

Lauyan Joe Cole Dean George ya bayyanawa kotun cewar dan kwallon bai sharara gudu ba, kuma na'urar da ta gano cewar yayi gudu nada 'yar matsala.