Liverpool ta sayi Brad Jones daga Middlesbrough

Jones
Image caption Liverpool ce kungiya ta shida da Jones zai kamawa gola

Liverpool ta kulla yarjejeniya da golan Middlesbrough Brad Jones akan pan miliyan biyu da dubu dari uku.

Dan shekaru 28 dai haihuwa,Jones ya sanya hannu a kwantiragin a ranar talata bayan an duba lafiyarshi.

Jones wanda dan Australia ne zai kasance mataimin Jose Reina wanda shine babban golan kungiyar.

A baya dai, Jones ya kamawa Middlesbrough kwallo a wasanni 75 kuma ya taba zuwa kungiyoyin Blackpool da Rotherham da Stockport da kuma Sheffield Wednesday a matsayin golan wucin gadi.