AC Milan na zawarcin dan kwallon Ghana Boateng

Boateng
Image caption Dan kwallon Black Stars Kevin Prince Boateng

Kungiyar AC Milan ta bayyana muradinta na sayen dan kwallon Ghana Kevin Prince Boateng daga kungiyar Portsmouth ta Ingila.

A halin yanzu Boateng na can Italiya inda ya fara shiga horo tare da sauran 'yan kwallon AC Milan kafin su sansanta akan batun kwangilar.

Kevin Prince Boateng dai ya kasance daya daga cikin matasan 'yan kwallon Black Stars na Ghana wanda suka haskaka a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

A baya Boateng yana bugawa Jamus kwallo a matakin 'yan kasada shekaru 21, kafin ya koma takawa kasar mahaifinshi kwallo wato Ghana.