Osaze Odemwingie ya koma West Bromwich Albion

Osaze
Image caption 'Yan Najeriya na kallon Osaze Odemwingie a matsayin dan kwallo mai kishi

Dan kwallon Najeriya Osaze Odemwingie zai koma kungiyar West Bromwich Albion daga Moscow Lokomotiv ta Rasha.

Odemwingie inda har aka gwada lafiyarshi zai kasance da West Brom na wucin gadi har zuwa shekara ta 2013.

Ya bugawa Najeriya kwallo a wasanni 51 kuma yace burinshi ya cika.

Osaze yace"Ba zan iya barin damar bugawa a gasar premier ba".

An haifi Osaze ne a garin Tashkent na Uzbekistan kuma mahaifinshi dan Najeriya ne sannan mahaifiyarshi 'yar Rasha.

A baya dai kungiyoyi kamarsu Blackburn Rovers da Bolton Wanderers duk sun nuna sha'awarsu akanshi.