Hodgson:Ba zamu saki Mascherano a kudi 'yan kadan ba

Mascherano
Image caption Kaptin din Argentina Javier Mascherano

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya hakikance ba zasu saki Javier Mascherano a kudi 'yan kadan ba.

Mascherano me shekaru 26, yana da sauran shekaru biyu kafin kwangilarshi ta kare a Anfield amma yanason ya tafi, kuma Inter Milan ta nuna sha'awarshi.

Amma Hodgson yace: "muna son tayin da muke tunanin yayi dai dai da darajar dan kwallon".

Akwai alamun cewar Mascherano yanason ya hade ne da tsohon kocinsa Rafael Benitez wanda ya bar Liverpool zuwa Inter Milan.