Mancini ya jinjinawa Balotelli

Mario Balotelli
Image caption Mario Balotelli

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya jinjinawa sabon dan wasan sa Mario Balotelli bayan dan wasan ya taimakawa kungiyar a nasarar datayi a gasar Europa.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 20 ya shigo wasan ne daga benchi inda ya zura kwallon dayan da Liverpool ta doke kungiyar Timisoara ta kasar Romania.

"Ya taka rawar gani a wasan shi na farko. Nayi kuma farin ciki ya zura kwallo. Dan wasan kwararre ne." in ji Mancini.

Balotelli ya koma kungiyar City ne daga Inter Milan a kudi fam miliyan 24.