An nada Francois Zahoui a matsayin kocin Ivory Coast

Ivory Coast
Image caption Tawagar 'yan kwallon Ivory Coast

An nada Francois Zahoui a matsayin kocin Ivory Coast wanda ya maye gurbin Sven-Goran Eriksson.

Dan shekaru 48, Zahoui ya dan shafe lokaci yana rikon mukamin, kuma shine ya jagoranci 'yan kwallon kasar suka doke Italiya daci daya da nema a makwanni biyun da suka wuce.

Sven-Goran Eriksson ne ya jagoranci tawagar Elephants din zuwa gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu amma sai suka kasa sasantawa da hukumar kwallon Ivory Coast bayan gasar.

Zahoui wanda bai goge a matsayin koci, ya kulla yarjejeniya ta shekaru biyu da kasar.

A farko wannan watan ne, hukumar kwallon Ivory Coast ta baiwa dan Faransa Gerard Gili mukamin amma sai yace akai kasuwa.

Aiki dake gaban Zahoui na farko shine karawa da Rwanda a ranar 5 ga watan Satumba a wasan neman tsallakewa zuwa gasar cin kofin Afrika a shekara ta 2012.