Jami'an FIFA na ziyarar gani da ido a Ingila

England 2018
Image caption Ingila na son FIFA ta bata dama a 2018

Jami'an hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA sun fara ziyarar kwanaki hudu a Ingila don gani da ido shirye shiryen da kasar keyi a yinkurinta na neman damar daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon duniya a 2018.

Za a duba filayen wasa da kuma gine gine a Manchester da London da Sunderland da Newcastle duk a wannan makon.

Tawagar jami'an FIFA din zasu tattauna da mataimakin Pirayi Ministan Birtaniya Nick Clegg kafin su duba filin wasa na Wembley tare da kocin Ingila Fabio Capello.

A ranar biyu ga watan Disamba ne za a sanar da kasashen da zasu dauki bakuncin gasar kwallon duniya na 2018 da 2022 a yayinda 12 ke takarar neman samun damar.

Ingila dai na fuskantar babban kalubale na samu wannan damar saboda jama'a na ganin cewar Rasha ce za ta samu damar.