Alex Ferguson ya soki 'yan kwallonshi

Ferguson
Image caption Sir Alex Ferguson ya ciji yatsa

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya soki 'yan kwallonshi bayanda suka sakacin tashi biyu da biyu tsakaninsu da Fulham a ranar Lahadi.

Bayan da United ke kan gaba daci biyu da daya sai Nani ya barar da penariti.

Ferguson ya shaidawa MUTV "idan ka samu damar samun nasara, ya kamata a zira penariti a raga"

Ferguson kuma ya nuna rashin gamsuwa akan dalilan da suka sanya aka bar Nani ya buga penariti din bayan Ryan Giggs na cikin fili.