Mauritania ta fice daga wasanni share fage na Afrika

Gabon Guinea
Image caption Kasashen Gabon da Guinea na jiran sauran Afrika a 2012

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta tabbatar da cewa kasar Mauritania ta fita daga cikin jerin kasashen da zasu buga wasannin share fage don neman buga gasar cin kofin kasashen Afrika a 2012.

Ficewar Mauritania ya nuna cewar za a samu sauyi akan yadda tsarin wasannin share fagen zasu kasance.

Mauritania dai na rukuni guda ne da kasashen Burkina Faso da Gambia da Namibia.

A ranakun 4-6 na Satumba ne za a fara wasanni share fagen gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a shekara ta 2012 a yayinda Gabon da Equitorial Guinea zasu dauki bakunci.