Manchester City ta lallasa Liverpool

Gareth Barry ne ya zura kwallon farko
Image caption Gareth Barry ne ya zura kwallon farko

Manchester City ta taka rawar gani a gaban mai kungiyar Sheikh Mansour a ziyararsa ta farko filin wasa domin kallon kungiyar.

Manchester City ta doke Liverpool ne da ci uku da nema.

Sheikh Mansour ya kashe makudan kudade domin siyo kwarrarun 'yan wasan zuwa kungiyar, kuma ga dukkan alamu kwaliya ta biya kudin sabulu saboda rawar da 'yan wasan suka taka.

James Milner wanda ya buga wasanshi na farko a kungiyar ne ya bawa Gareth Barry fassing din kwallon daya zura sannan kuma Carlos Tevez ya zura ta biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Tevez dai ya samu bugun fenariti inda ya zura kwallo ta uku, inda kuma aka tashi wasan babu ci.