Fulham ta sayi Halliche

Rafik Halliche
Image caption Rafik Halliche

Fulham ta bada sanarwa siyan dan wasan Algeria Rafik Halliche daga kungiyar Benfica na tsawon shekaru uku.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 23 ta takawa Algeria leda a duka wasannin data buga a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu.

"Ina matukar farin ciki da komawa Fulham". Inji dan wasan a bayanin da ya yi wa shafin intanent din Fulham.

"Wannan dama ce da aka bani inyi gogoyya da shaharrarun 'yan kwallo a gasar Premier, kuma ina alfahari da yin hakan".

Halliche ya bugawa Algeria wasa sau 20 tun bayan da ya fara buga mata a karawar da kasar ta yi da Senegal a shekarar 2008.