Hodgson:Dole se Barca ta biya makudan kudade akan Mascherano

Mascherano
Image caption Dan kwallon Argentina Javier Mascherano

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya ce dole ne sai Barcelona ta kara kudi akan tayin data yi na Javier Mascherano.

Mascherano me shekaru 26 da haihuwa, baya cikin tawagar 'yan kwallon Liverpool wadanda suka sha kashi wajen Manchester City daci uku da nema a ranar Litinin.

Hodgson ya shaidawa BBC cewar "Barcelona ta juya mai kai, kuma sun hanashi zama".

Kocin Barcelona Pep Guardiola yace "sai Mascherano yazo Catalon kafin mu kamalla yarjejeniya".

Hodgson ya ce tayin da Barca tayi ya yi kasa, a yayinda rahotanni ke nuna cewar Liverpool na bukatar pan miliyan 25 akan Mascherano.

Wasu rahotannin sun wallafa cewar Barca na son biyan pan miliyan 12 akan dan kwallon da Liverpool ta siya pan miliyan 18.