Aquilani ya koma Juventus daga Liverpool

Alberto Aquilani
Image caption Alberto Aquilani

Dan wasan Liverpool Alberto Aquilani ya koma Juventus na wucin gadi.

Kungiyar Juventus ta Serie A ta sayi dan wasan ne na wucin a kan kudi fam miliyan 13.

Liverpool dai ta bari dan wasan ne ya nemi wata kungiya, bayan ya kasa taka rawar gani tun da ta sayo shi daga Roma a kan fam miliyan 17 a kakar wasan bara. Tsohon kocin Liverpool Rafeal Benitez ne ya sayi dan wasan mai shekarun haihuwa 26, bayan da Xabi Alonso ya koma Real Madrid.