Gago ba zai taka leda na wata guda

Dan wasan Real Madrid Gagp ba zai samu damar taka leda ba na tsawon wata guda bayan raunin da ya samu.

"Dan wasan dai ya turgude gwiwarsa ne." In ji wata sanarwa da kungiyar Madrid ta bayar A yanzu haka dai Gago ya shiga cikin sahun su Pepe da Ezequiel Garay da Raul Albiol da kuma Kaka wadanda ke jinyar rauni a kungiyar ta Madrid.