Capello ba zai kai Ingila ko ina ba- In ji Mourinho

Jose Mourinho
Image caption Jose Mourinho

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce Ingila ba za ta lashe wata babban gasa ba karkarshin jagoranci Kocin tawagar kasar Fabio Capello.

Mourinho ya ce Capello bai iya tafiyar da 'yan wasa ba, saboda yana yawan yi musu ihu.

" Idan kana yiwa 'yan wasa ihu, bazasu saki jikinsu, su taka leda ba, zasu rika wasa ne cikin tsoro". In ji Mourinho.

"A lokacin ma da ya hori kungiyar Madrid haka ya tayiwa 'yan wasan".

Mourinho ya ce kamata ya yi a rika lallashin 'yan wasa domin su saki jikin su, kuma su buga abin da mai horaddasu ya ke so.

A baya dai an soki kocin Ingila Fabio Capello saboda mummunar rawar da kasar ta taka a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu.