Semenya za ta yi takara a wasanni Commonwealth

Caster Semenya
Image caption Caster Semenya

'Yar tseren mita dari takwas din kasar Afrika ta kudu Caster Semenya za ta yi takara a wasanni Commonwealth da za'a yi a birnin New Delhi a Indiya.

'Yar tseren mai shekarun haihuwa 19 ta dawo tsere ne a watan Yulin bana bayan ta debe watanni takwas tana hutu saboda gwaje-gwajen jinsi da ake yi mata.

An dai yi zargin cewa dai Semenya maza, mata ce.

Amma bayan ta dawo Semenya ta lashe tseren uku da ta yi takara.

"Muna matukar farin ciki ta dawo tsere kuma ga dukkan alamu muna da kwarin gwiwa cewar za ta taka rawar gani a wasanni." In ji Shugaban kula da wasanni Olympic na kasar Afrika ta kudu Cif Gideon Sam.