An zabi Aminu Maigari a matsayin shugaban NFF

Super Eagles
Image caption Super Eagles ta sha kashi a Afrika ta Kudu

An zabi Alhaji Aminu Maigari a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF.

Zaben da aka gudanar a Abuja an yi shi cikin kwanciyar hankali da lumana.

Tsohon dan kwallon Green Eagles Segun Odegbami bai shiga cikin zaben saboda ya gabatarda kara gaban kuliya.

Maigari ya kasance shugaban riko na NFF bayan an tsige Sani Lulu sakamakon taka mummunar rawar da Super Eagles tayi a Afrika ta Kudu.

Daya daga cikin 'yan takarar kujerar shugaban kungiyar Shehu Dikko ya ce baida matsala da zaben, duk da cewar ya fadi kuma yana fatar matakin zai kai kasar ga cigaba a fannin kwallon kafa.