Ba za ayi amfani da na'urar fasaha ba a kwallo-Platini

Platini
Image caption Shugaban UEFA Platini

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai,UEFA Michel Platini ya ce alkalan wasa basa bukatar fasahar na'urar bidiyo don yanke hukunci a kwallon kafa.

A cewar shi amfani da alkalan wasa biyar sun isa a gano taba kwallo da hannu ko kuma kwallon ya wuce layi.

An dai samu kura kurai da dama a lokacin gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu wajen tabbatar da shigar kwallo a raga,abinda kuma ya sanya aka yita kiraye kirayen kawo na'urar fasaha ciki alkalancin kwallon kafa.

Platini yace"idan har aka kara alkalan wasa tabbas zasu yi aiki kamar na'urar fasaha".

A halin yanzu dai masana harkar kwallon kafa na ganin cewar tuni ya kamata FIFA ta bullo da tsarin amfani da fasahar.