Ba sunnan Ballack a tawagar Jamus

Micheal Ballack
Image caption Ballack na daga kofi a lokacin da yake kungiyar Chelsea

Kocin Jamus Joachim Loew ya cire sunnan kyaftin din kasar Michael Ballack a cikin 'yan wasan da za su taka leda a wasanni share fage na taka leda a gasar cin kofin Turai.

Kocin dai ya bai sanya sunnan Ballack mai shekarun haihuwa 33 a cikin 'yan wasan da za su kara da Azerbaijan a ranar 3 ga watan Satumba ba. Har yanzu dai Ballack na murmurewa sanadiyar raunin da ya samu a kafar sahunsa a lokacin dayake takawa Chelsea leda a watan Mayu.

A cikin wata sanarwa Loew ya ce: "Michael yana ci gaba da murmurewa kuma kamata ya yi mu bashi lokaci saboda muna da matasan 'yan wasa".

Philipp Lahm wanda ya zama kyafin din tawagar kasar a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu zai ci gaba da zama kyaftin din kasar a madadin Ballack.

Ballack dai ya fara horo da sabuwar kungiyarshi ta Leverkusen a Jamus.

Tawagar Jamus

Masu tsaron gida: Manuel Neuer (Schalke 04), René Adler (Bayer Leverkusen), Tim Wiese (Werder Bremen) 'Yan wasan baya: Holger Badstuber (Bayern Munich), Marcell Jansen (Hamburg), Philipp Lahm (Bayer Munich), Per Mertesacker (Werder Bremen), Sascha Riether (Wolfsburg), Heiko Westermann (Hamburg)

'Yan wasan tsakiya: Sami Khedira (Real Madrid/ESP), Toni Kroos (Bayern Munich), Marko Marin (Werder Bremen), Mesut Ozil (Real Madrid/ESP), Bastian Schweinsteiger (Bayern Munich), Christian Trasch (Stuttgart)

'Yan wasan gaba: Cacau (Stuttgart), Mario Gomez (Bayern Munich), Stefan Kiessling (Bayer Leverkusen), Miroslav Klose (Bayern Munich), Thomas Müller (Bayern Munich), Lukas Podolski (Cologne)