Meireles ya koma Liverpool

Liverpool ta sayi dan wasan Portugal Raul Meireles na tsawon shekaru hudu daga kungiyar Porto.

Liverpool ta sayi dan wasan mai shekarun haihuwa 27 a kan fam miliyan11.5

Kungiyar dai ta sayi dan wasan ne domin ya maye gurbin Javier Mascherano, wanda ke shirin komawa kungiyar Barcelona.

"Liverpool tana da dimbin tarihi, koma ina matukar farin cikin taka mata leda." In ji Meireles

" Ya dade ina neman in taka leda a Ingila, a yanzu haka dai haka ta ta cimma ruwa."