Sunderland ta doke Manchester City

Darren Bent ne ya zura kwallon a bugun fenarity
Image caption Darren Bent ne ya zura kwallon a bugun fenarity

Sunderland ta yi galaba a kan kungiyar Manchester City da ci daya mai ban haushi.

Darren Bent ne ya zura kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Sunderland dai itace kungiyar farko data zura kungiyar Manchester City leda a kakar wasanni bana.

Kungiyar City dai ta kashe makuden kudade domin siyan 'yan wasa a bana.