JS Kabylie ta haskaka a Afrika

Caf
Image caption Tambarin hukumar kwallon Afrika CAF

Kungiyar JS Kabylie ta Algeriya ta kasance ta farko data samu gurbi a zagayen kusada karshe na gasar zakarun kwallon Afrika a bana bayan ta buga kunen doki tsakaninta da Al Ahly ta Masar.

'Yan Masar wanda ke gida na bukatar nasara don yin matsin lamba ga bakin inda Mohamed 'Geddo' Nagy ya zira kwallon farko a ragar Kabylie minti 22 da fara wasan.

A yayinda shi kuma Saad Tedjar ya farke kwallon.

Sakamakon ya nuna cewar Kabylie nada mako goma a inda Al Ahly keda maki biyar a yayinda rage wasannin biyu a rukunin B.

Tsakanin Ahly ko Heartland ta Najeriya, daya daga cikinsu za ta hade da Kabylie don tsallakewa daga rukunin.

Ita dai Heartland a karshen mako ta doke Ismaili daci biyu da daya abinda kuma ke nufin cewar Heartland nada maki hudu sai Ismaili me maki uku.

A rukunin A, mai rike kofin wato kungiyar TP Mazembe ta Congo ta sha kashi wajen Esperance ta Tunisia daci uku da nema.

Sai kuma Dynamos ta Zimbabwe wacce itama ta samu galaba akan Entente Setif daci uku da nema.