Dan kwallon Sierra Leone Mohammed Kallon ya samu rauni

Kallon
Image caption Dan kwallon Sierra Leone Mohammed Kallon

Dan kwallon Sierra Leone Mohammed Kallon ba zai takawa kasarshi leda ba a wasanta na share fagen buga gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a shekara ta 2012.

Dan shekaru talatin da haihuwa, Kallon ba zai buga wasa tsakaninsu da Masar ba saboda rauni.

A cikin jerin da kocin kasar Christian Cole ya fitar, goma sha biyar daga ciki a Turai suke taka leda.

Kallon ya shaidawa BBC cewar"na yanke shawarar kin buga kwallon tsakaninmu da Masar saboda bana jin dadi".

Ya koma kungiyar Shaanxi Chanba ta China a watan Fabarairu kuma ya zira kwallaye biyar cikin wasanni 14 daya buga kawo yanzu.